Hakkin mallakar hoto Getty Images

Nicki Minaj ta ce ta yanke hukuncin "yin ritaya daga waka don samun iyali" - ta kuma shaida wa magoya bayanta cewa tana son su "har abadan"

Mawakiyar wacce ta taba shiga gasar Grammy har sau 10 ba tare da nasara ba, tana soyayya da wani mutum mai suna Kenneth Petty ta kuma nuna alamar cewa za su yi aure.

Baya ga yin wakoki, matashiyar, mai shekara 36, ta kuma fito a fina-finan Hollywood da dama tana kuma gabatar da wani shiri nata na kanta a gidan rediyo.

Ba ta yi karin bayani kan ko za ta yi ritayar ne a dukkan bangarorin da take aiki ba, ko kuma ma idan da gaske take yi.

Bayan da ta saki wasu jerin wakoki a shekarar 2000, fitacciyar mawakiyar gambarar zamani, Nicki Minaj ta shiga kamfanin wakoki na 'Young Money' mallakin mawakinnan na Hip Hop, Lil Wayne.

Kundin wakokin da ta fara fitarwa shi ne 'Pink Friday' wanda ya fito cikin shekarar 2010.

Wakokinta irinsu Super Bass da Anaconda da Starships su ne suka fito da ita a wannan harka ta wakar Hip Hop har ta zama daya daga cikin shahararrun mata masu wakar gambarar zamani a duniya.

Wakokin da ta yi ita kadai sun sa ta samu miliyoyin daloli, sai dai akwai wakoki da dama da ta yi da fitattun mawaka irinsu Ludacris da Usher da David Guetta da Madonna da Ariana Grande da Kanye West da Justin Bieber da kuma wasu wakoki da dama.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

An sha zabar ta domin samun babbar kyauta a harkar wakoki ta Grammys har sau 10, inda ta samu nasarar lashe kyaututtuka biyar na wakokin bidiyo.

Sannan ta yi shura cikin jerin wakoki 100 da wata mawakiya ta taba rerawa a tarihi.

Baya ga waka, Nicki Minaj ta fito a fina-finai da suka hada da 'The Other Woman' da 'Ice Age: Continental Drift'.

Sai dai a shekarar 2018 ne, karsashin da Nicki take da shi a harkar waka ya disashe, inda kundin wakokinta na hudu mai taken 'Queen' bai yi farin jinin zama kan gaba ba a Amurka.

Hakan ya fusata ta har ta caccaki manhajar wallafa wakoki ta Spotify da kuma mawaki Travis Scott wanda kundin wakokinsa ya zama na daya.

Daga nan ne ta soke wani shirin gudanar da taron shakatawa a daukacin yankin Arewacin Amurka da mawaki, Future.

Sai dai ta ce ta soke shirin kawai domin ba ta da lokacin shiryawa taron yadda ya kamata, ta yadda zai burge masu kallo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A hannu guda kuma, akwai wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba da ke cewa soke taron ya faru ne sakamakon rashin tururuwar jama'a wajen sayen tikitin kallon taron na su.

Nicki Minaj ta fitar da wata sabuwar waka a watan Yuni, sannan ana tunanin tana kokarin sakin wani sabon kundin wakoki.

Shahararriyar mawakiyar ta fito ta fadi gaskiyar al'amarin da wannan sanarwar barin harkokin waka kasancewar an santa da rashin tsoro kuma mai fadar ra'ayinta gaba-gadi a wasu lokutan masu sarkakiya.

Kuma wannan sanarwar ba za ta zowa da dimbin magoya bayanta da mamaki ba, saboda akwai jita jitar da ke cewa ai tuni Nicki ta yi auren sirri da Kenneth Petty.