Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ya zuwa daren Talata, an samu karin mutum 32 da suka kamu da cutar sarkewar numfashi ta korona a jihar.

Hakan na nufin adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 397 tun bayan bullar cutar a jihar.

Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,226 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 307.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa, kuma ci gaba da gwaje-gwaje a jihar bayan an sami tsaiko ya sa an sami karuwar yawan wadanda ke dauke da cutar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
  • Coronavirus: Yadda cutar ta bulla Jihar Kano
  • An yi feshin magani a wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano
  • Coronavirus: Mece ce ita da kuma asalinta?
  • Coronavirus: BBC ta amsa tambayoyin da kuka aiko

Alkaluman mutum 32 da hukumar NCDC ta fitar a daren Litinin na wadanda suka kamu da cutar na nuni da yadda annobar ke kara bayyana a jihar ta Kano.

A yanzu dai cutar na kara bazuwa a jihohin da ke makwabtaka da Kano - Katsina na da mutum 92 sai Jigawa mai mutum 39, Bauchi na da 83 yayin da Kaduna kuma ta ke da mutum 84.

A cewar sanarwar da hukumar NCDC ta fitar a Twitter, zuwa daren Talata, mutum 2,950 ne suka kamu a jihohi 34 har da Abuja. Daga cikin adadin, 481 sun warke har ma an sallame su daga asibiti.

Sai dai adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya karu, inda jimilla mutane 98 suka rigamu gidan gaskiya.